Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yansanda Sun Hana Gwamnan Rivers Shiga Gidan Gwamnati


Gwamna Ameachi na Jihar Rivers
Gwamna Ameachi na Jihar Rivers

Yayin da ya dawo daga rangadin wasu sassa a jiharsa 'yansanda rike da makamai sun hana gwamna Ameachi na jihar Rivers shiga gidan gwamnati.

Bayan rangadin ayyukan raya kasa a jiharsa gwamnan jihar Rivers Ameachi ya dawo gida da tawagarsa amma wasu 'yansanda rike da makamai sun hana shi shiga gidan gwamnati.Kokarin da gwamnan ya yi na anfani da wata karamar kofa ya citura.

Bayan wata 'yar turka-turka gwamnan ya shiga gidan ta baya. 'Yansanda sun ce sun dauki matakin ne sabili da wani umurni da aka basu daga sama cewa kada su barshi ya shiga gidan gwamnati.

Wani dan jihar Rivers ya ce abun dake faruwa cigaba ne na gwagwarmayar siyasa dake tsakanin gwamnan da 'yan siyasar jihar dake Abuja. Dama bangaren gwamna Ameachi da rundunar 'yansandan da Mbu ke shugabanci a jihar ba'a ga maciji. Wani kuma ya ce lamarin bashi da kyau ga kuma taka doka da 'yansanda suka yi.

To sai dai mai magana da yawun 'yansandan jihar Rivers DSP Angela Agabi ta ce zargin da ake yiwa rundunarsu ko kadan ba haka ba ne.

Lamido Abubakar Sokoto nada rahoto.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG