Akalla 'Yansandan Msar 54 ne aka kashe a lokacinda suka kai wani somame a maboyar mayakan sakai kusa da birnin Alkahira, kamar yadda jami'an tsaron kasr suka yi bayani.
Jami'an wadanda suka nemi a sakaye sunayensu sun ce an yiwa jami'an tsaron kwanton bauna nea daren jiya jumma'a, bayan suka hallara a mafakar 'yan binidgar dake yankin hamada dake yammacin kasar da ake kira al-Bahriya.
Jami'ai 20 da kuma kurata 34 suna daga cikin wadanda suka halaka a harin. Ma'aikatar harkokin cikin gida a sanarwar da ta bayar tace wasu jami'anta sun yi shahada, sai dai bata bada karin bayani ba
Facebook Forum