Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen Libiya Sun Sake Kwace Garin Bisa Tudu Da Ke Yamma


Yadda NATO ke ta barin wuta a Libiya
Yadda NATO ke ta barin wuta a Libiya

‘Yan tawayen Libiya sun ce sun kwace garin Yafran na bisa kan tudu da ke yammacin kasar daga dakarun da ke biyayya ga shugaba Muammar Gaddafi

‘Yan tawayen Libiya sun ce sun kwace garin Yafran na bisa kan tudu da ke yammacin kasar daga dakarun da ke biyayya ga shugaba Muammar Gaddafi bayan hare-haren da NATO ta kai ta jiragen sama sun lalata wasu muhimman cibiyoyin sojin gwamnati, wanda hakan ya bayar da dama ga ‘yan tawaye ta dannawa gaba.

Mayakan kabilar Asbinawa, wadanda su ka shiga sahun masu yaki da gwamnati, sun sake kwace Yafran mai nisan kimanin kilomita 100 daga kudu maso yammacin birnin Trabulus ranar Litini. Dakarun da ke biyayya ga Gaddafi sun kai hari kan yankin tuddan da ke yamma bayan da ‘yan kabilar Asbinawa suka kalubalanci dakarun gwamnati a farkon zanga-zangar ta kin gwamnati.

Rahotannin kafafen yada labarai sun ce dakarun gwamnati sun bar garin kuma ana ma iya hangen tutocin ‘yan tawayen kafada da kafada da yagaggun hotunan Mr. Gaddafi. Ran Alhamis da ta gabata, jiragen saman yakin Burtaniya sun lalata tankokin yaki biyu na gwamnati da kuma mayan motocin da ke dakon manyan kayan fada a Yafran.

An cigaba da kokarin bin hanyar diflomasiyya a yau Talata, saboda manzo na musamman da shugaban Rasha Dmitry Medvedev ya turo na shirin ganawa da jami’an Majalisar Wucingadi ta Shugabancin Kasa da ke birnin Benghazi da ke gabashin kasar.

Ma’aikatar Harkokin Wajen China ta ce daya daga cikin jami’an diflomasiyyarta da ke Misra shi ma ya gana da ‘yan tawayen kwanan nan. Ma’aikatar ta fadi a wani bayanin da ta yi yau Talata cewa Ministan Harkokin Wajen Libiya zai kai ziyarar kwanaki uku zuwa China, to amman bai bayar da cikakken haske game da ziyarar ba.

Da China da Rasha duk sun kaurace lokacin da Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ta kada kuri’a a watan Maris ta shata sararin da za a haramta wa jiragen saman Libiya ratsawa, kuma sun yi ta kiran da a tattauna kan rikicin.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG