Mutane akalla 14 sun mutu wasu kuma 29 sun samu raunuka a jiya Laraba, bayan da wasu ‘yan kunar bakin wake su hudu su ka kai hari a Maiduguri, hedikwtar Jahar Barno mai fama da tashin hankali a Najeriya.
Maza biyu da mata biyu ne su ka tarwatsa kansu a unguwar Muna da ke cikin birnin na Maiduguri, wanda ya zama tamkar cibiyar fafatukar tsattsauran ra’ayin nan na Boko Haram.
Kakakin Rundunar ‘Yansanda Victor Isukwu, ya ce maza biyu da mata biyun, sun auna sassan birnin ne da aka fi samun cinkoson jama’a.
Haka al’umarin ya kasance a jihar Adamawa, domin kwana kwana nan ‘yan bindiga masu tada kayar baya suka kai hari a garin Gulak hedkwatar karamar hukumar Madagali a jihar Adamawa, sai gashi an kwashe daren Laraba ana bata kashi tsakanin jami’an tsaron Najeriya da ‘yan ta’addan a yankin Sabon Garin Madagalin.
Rahotannin na cewa mayakan na Boko Haram sun yi dirar mikiya ne a yankin Sabon Garin na karamar hukumar Madagali wanda kuma har cikin dare an ta musayar wuta a tsakanin jami’an tsaro da yan bindiga, kamar yadda shugaban karamar hukumar Madagali Yusuf Muhammad ya tabbatar wa wakilin sashen Hausa a cikin dare.
An kai wannan harinne a kasa da mako guda da wani yunkurin da yan Boko Haram suka yi na kwace Gulak, hedikwatar karamar hukumar Madagalin, batun da yasa majalisar wakilai kada kudurin kai Karin jami’an tsaro zuwa yankin. Mr Adamu Kamale shi ke wakiltar al’umman Madagali da Michika a majalisar wakilai ya nuna kaduwarsa da wannan harin da aka sake kaiwan.
Shima dai gwamnan jihar Adamawa Sen.Muhammadu Bindow Umaru Jibrilla wanda ya tabbatar da wannan sabon harin, ya bukaci al’ummomin yankin ne da su kwantar da hankilansu indaya yaba da jajircewan da jami’an tsaro suka yi a wannan karon.
Kawo yanzu dai hukumomin tsaro basu bayyana alkalumman wadanda harin ya rutsa da su ba ko suka rasa rayukansu, yayin da aka ce jama’a da dama basu kwana a gidajensu ba, sabili da gudun abun da ka iya faruwa.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani
Facebook Forum