Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan sandan Kamaru Sun Tarwatsa Masu Sallar Juma’a


Musulmi suna sallah a masallacin Maroua da ke kasar Kamaru
Musulmi suna sallah a masallacin Maroua da ke kasar Kamaru

Jami’an tsaro a kasar Kamaru sun tarwatsu wasu masu ibada da suka taru domin gudanar da sallar Juma’a.

Lamarin ya faru ne yayin da al’umar Musulmi suka fara azumin watan Ramadana wanda ya yi kicibis da ranar ta Juma’a.

Hakan kuma ya saba dokar hana fita da taron jama’a da hukumomin kasar suka ayyana domin dakile yaduwar cutar coronavirus.

Wata sanarwa da ‘yan sanda kasar suka fitar ta ce, an tarwatsa taron masallatan ne a masallatai 13 da ke Yammaci, Tsakiya da kuma Arewa mai nisa.

Rahotanni sun ce Jama'a a wadannan yankunan sun nace sai sun yi sallah a lokacin Ramadana duk da cewa hukumomi sun hana.

Akalla mutum 1,300 aka tabbatar suna dauke da cutar a kasar ta Kamaru kana wasu 43 sun mutu.

Kamaru ita ce kasar da ta fi yawan masu dauke da COVID-19 a yankin tsakiyar Afirka.

Limamin wani masallaci a yankin Koza, daya daga cikin yankunan da aka tarwatsa masu sallar, Imam Dairou Abdoullahi ya ce mutanen kauyen suna ikrarin cewa cutar ba ta bulla a yankin ba.

Amma ya ce duk da haka, akwai bukatar mutane su bi umurni su zauna a gidajensu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG