A makon da ya gabata ne aka gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa a Najeriya.
Yayin da hukumar zabe ta INEC ta tabbatar da Janar Mohammadu Buhari mai ritaya a matsayin zababben shugaban kasa, al’ummar jihar Kano sun bayyana jin dadinsu akan yadda shugaba Goodluck Jonathan ya amince da sakamakon ba tare da wata rigima ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jiyar Kano ASP Magaji musa Majiya, ya fadi cewa a zaben bana ba a sami masu akaita laifuka da tashe-tashen hankali da yawa ba. Ya shaida hakan ne a wata hira da wakiliyar Dandalin VOA Baraka Bashir .
Magaji Majiya Ya kara da cewa laifufukan da aka aikata a jihar baki daya guda ashirin da daya ne wanda suka hada da tada zaune tsaye, tunzara tada hankali, mallakar katin zabe ba bisa ka’ida ba, yin barna, amfani da gwada karfi, mallakar makamai da sauransu.
ASP Magaji ya kuma fadi cewa sun iya kwato makamai da wasu abubuwa da dama daga hannun masu laifin ciki harda gorori 78, wukake 16, adduna 31, da takobba 4, kibiyoyi, danko, gatari da ganyen wiwi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan ya kara da jan kunnen matasa da su kaurace wa duk wani tashin hankali a zaben gobe don ‘yan sandan jihar Kano a shirye suke.