Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda a Najeriya Sun Nuna Damuwa Kan Yadda Ake Amfani Da Kayansu Domin Yin Fashi


Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Abubakar Adamu
Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Abubakar Adamu

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta nuna damuwa game da yadda wasu bata gari kan saje suna sa kayan 'yan Sintiri da na 'yan banga domin yin fashi da kuma ayyukan tu'annati.

Lamarin wanda ya fi kamari a yankin arewa maso gabashin Najeriya na ci gaba da tayar da hankulan jama'a.

To sai dai kuma, sakamakon wannan sabon salo, ya sa rundunar ta 'yan sandan Najeriya daukar mataki, na gargadi ga kungiyoyin sintiri da maharba, musamman na yadda kungiyoyin yanzu ke saka kaya kamar na jami'an tsaro tare da rike makamai ba bisa ka'ida ba.

DSP Suleiman Yahya Nguroje, shi ne kakakin rundunar 'yan sandan jihar Adamawa, kuma ya yi wa Muryar Amurka karin haske game da matakan da suke daukawa domin magance wannan matsalar.

"Mun fitar da sanarwar hana duk wasu kungiyoyin 'yan banga saka kayan da suka yi kama da na jami'an tsaro domin mutane su iya bambantawa tsakanin jami'an tsaro da saura. Duk da cewar 'yan banga da sauransu na kokari matuka, amma ana yawan samun kura-kurai da ke janyo matsaloli," in ji DSP Nguroje.

Matsalar tsaro dai na ci gaba da ta'azzara a wasu jihohin Najeriya, lamarin da ya janyo al'umma suka kafa kungiyoyin sakai na 'yan Sintiri.

Saurari cikakken rahoton a cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG