Rachel Whalen, na tsinci kaina cikin mawuyacin hali matukar gaske, a lokacin da nake makarantar sakandire, domin kuwa abokai sun ci zali na ta kafar sadarwar zamani, har wani lokaci suke rubuce-rubuce da suka sani cikin damuwa.
Wanda har wasu lokutta na kanji kamar na kashe kaina, don ba wanda ke sona a duniya. Amma daga bisani na samu taimako, wanda hakan yasa na takaita yadda nake amfani da duk wasu kafafen sadarwar zamani.
Binciken da hukumar ilimi da fashin baki ta fitar, ya nuna cewar mata na fuskantar cin zarafi a kafafen sadarwar zamani, fiye da yadda maza ke fuskanta. Sau da yawa maza da ke cin zarafin ‘yan mata a shafukan zumuntar yarna gizo, ba komai ke sa su yin hakan ba, illa neman a kulasu.
Wani sabon mataki da wasu makarantu suka fara dauka yanzu shine, na horas da duk wani dalibi da aka samu da raina ‘yan mata a shafukan yanar gizo, kuma basu tsaya nan kawai ba, harma zasu dauki wasu matakai da suka wuce hakan, don tabbatar da cewar an kawo karshen cin zarafin ‘yan mata a kowane hali.
A yanzu haka ma, har wasu jihohin Amurka sun dauki wasu dokokin ladabtarwa ga duk wanda aka samu da irin wadannan muggan dabi’un, jihar Texas da California a cikin ‘yan shekarun nan suke kan gaba wajen aiwatar da wannan dokar.
Facebook Forum