Masu fashin baki sun dade su na bayyana cewa labaran karya da na batanci sun zama ruwan dare a cikin al’umma, lamarin da ke sanya kiyayya a zukatan mutane ya kuma haifar da tashin-tashina. A ‘yan shekarun nan, an rasa rayuka da dukiyoyi masu dimbin yawa a Najeriya da ma wasu kasashen Afurka a bisa wannan dalili.
Wannan ya sa Cibiyar Fasahar Sadarwa Da Ci Gaban Jama’a wato Centre For Information Technology and Development (CITAD), tare da hadin gwiwar hukumar tallafa wa kasashe ta kasar Amurka, USAID, suka shirya wani taron bita ga yan jarida da kuma masu ruwa da tsaki a Jihar Adamawa don kauce wa rahotonnin da za su iya haifar da kiyayya, wato Hate Speech.
Masana da suka gabatar da makala a wajen taron, sun tabo batun illar yada rahotonin karya da kalaman batanci, kamar yadda wasu kafafen sadarwa ke yi, kana, cibiyar ta bayyana bukatar da ke akwai ga ‘yan jarida na hada hannu domin dakile wannan lamarin da ke kawo wa Najeriya ci baya.
Yada labaran karya a cikin al’umma musamman ma a kafafen sadarwa yana matukar sanya jamma’a cikin firgici da tashin hankali.
Ga Ibrahim Abdul-Azeez da cikakken rahoton:
Facebook Forum