Hukumomin Najeriya sun bada labarin mutane da ake zargin ‘yan tsagera ne masu da’awar addini sun kai hari kan ofishin ‘Yansanda da rassan bankuna biyu a arewa maso gabshin kasar, suka kashe akalla mutane 12.
Jami’ai suka ce jiya Alhamis maharan suka dira kan garin Gombi dake jihar Adamawa, farko suka kai harin bam kan ofishin sanda daga bisani kuma suka afkawa rassan bankunan First Bank da na UNION dake garin.
‘Yansanda suka ce akalla an kashe ‘yansanda hudu, soja daya, da kuma ma’aikatan banki bakwai a lokacinda aka kai wan nan hari. Suka ce maharan sun tsere da kudade daga Bankunan da ba’a bayyana yawansu ba.
‘Yansand a suna aza laifin kisan kan kungiyar Boko Haram, wacce ta juma galibi tana kai hare hare arewa maso gabashin kasar, kan ‘yansanda, ‘yan siyasa da shugabannin addini.
Ahalin yanzu kuma kungiyar rajin kare hakkin Bil’adama Human Rights Watch mai cibiya anan Amurka tana zargin hukumar EFCC ta Najeriya da kasa yin kome wajen hana manyan ‘yan siyasa kasar da suka aikata rashin gaskiya cin Karensu babu babbaka.
Cikin rahoto da ta sake jiya Alhamis kungiyar tana zargin hukumar EFCC Da rashin tasiri sabo da rashin kan gado, cuwa cuwa a hukumar da kuma katsalandan daga ‘yan siyasa.