Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Sake Kai Wani Mummunan Hari a Somaliya


Shugaban Somaliya Mohammed Abdullahi Mohammed Farmajo
Shugaban Somaliya Mohammed Abdullahi Mohammed Farmajo

Mugunyar kungiyar nan ta Taliban ta sake kai wani hari a Mogadishu babban birnin kasar Somaliya, inda su ka kashe mutane da dama

Mutane sama da 15 aka kashe wasu kuma sama da 24 aka raunata, a wasu hare-hare biyu da aka kai jiya Asabar a rukunin ginin da ke kunshe da Ma'aikatar Cikin Gida da Ma'aikatar Tsaro da ke Mogadishu babban birnin kasar Somaliya a cewar shaidu.

Hari na farko ya auku ne lokacin da wasu 'yan bindiga su tayar da wasu manyan bama-bamai a mashigar Ma'aikatar ta Cikin Gida kafin wasu mayaka uku su ka abka ciki. An ga hayaki na ta tashi a wurin.

Shaidu sun ce su ma jami'an tsaro sun kaddamar da hare-haren taka ma mayakan burki, inda su ka kwashe sa'a guda su na ta musayar wuta da mayakan kafin su ka yi nasarar shawo kan mamayar, su ka kuma kashe mayaka ukun duka.

Shaidu sun ce daga cikin wadanda aka kashe a hari na farkon har da ma'aikatan gwamnati.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG