Hukamomi sun ce wasu mutane su 10 sun ji jikkata a harin da aka kai kan ginin Ma’aikatar Ilimi a Jalalabad, babban birnin lardin Nangarhar. Jami’an tsaro sun yi musayar wuta na lokaci mai tsawo da maharan kafin suka fatattake su.
Wannan shine mummunan hari na biyu da ya faru a Jalalabad cikin yan kwanakin nan. An kashe wasu mutane 10, wasu su 4 kuma sun jikkata jiya Talata a lokacin da wani dan kunar bakin wake ya tada nakiyoyin da yayi dammara da su a wajen wan ishingen binciken jami’an tsaro.
Kungiyar Taliban da yan bindigar da ke da alaka da ISIS na da karfi a yankin Nangarhar, kuma sun sha daukar alhakin kitsa hare-haren bom akan dakarun gwamnati.
Facebook Forum