Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Akan Ofishin Jakadancin Indiya


​A Afghanistan wasu yan bindiga dauke da makamai sosai sun budewa ofishin jakadancin Indiya a yammaci kasar wuta a yau juma'a, to amma dukkan ma'aikatan jakadancin sun tsalaka rijiya da baya domin babu wanda yaji rauni.

Hukumomi a Afghanistan sunce wasu mutane hudu dauke da bindigogi masu sarafa kansu da gurnati da ake harbawa da roka ne suka kaddamar da wannan hari a birnin Herat daga wani gini dake kusa, suka hadasa musayar harbe harbe tsakaninsu da jami'an tsaro. 'Yan sanda sunce an kashe dukkan yan bindigan guda hudu.

A can birnin New Delhi kasar Indiya kuma, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Syed ya fadawa kafofin yada labaru Indiya cewa yan sandan dake tsaron kan iyakar kasar da Tibet sun samu nasarar dakile harin kafin isowar jami'an tsaron kasar Afghanistan.

Nan da nan babu kungiyar data yi ikirarin cewa ita keda alhakin kai harin.

Ofishin Prime Ministan Afghanistan yace ya yiwa Prime Ministan Indiya mai jiran gado Narendra Modi bayanin al'amarin ta wayan tarho da kuma yadda jami'an tsaron Afghanistan suka yi saurin kai taimako kuma ya tabbatarwa Prime Ministan cewa za'a kare yan Indiya dake kasar kuma babu wanda yaji rauni a harin.
XS
SM
MD
LG