WASHINGTON, DC —
'Yan sandan kasar Iraqi sun ce 'yan bindiga sun kama wani babban dan siyasar Baghadaza dan Sunni.
'Yan sanda sun ce da yammacin jiya jumma'a aka yi gaba da Riyadh al-Adhadah, wanda likita ne kuma shugaban majalisar lardin Baghadaza. Wasu 'yan bindiga cikin bakaken motoci 10 kirar jeep su ne su ka tafi da shi.
Nan take babu tabbas ko jami'an tsaro ne suka kama Adhadah ko kuma sace shi aka yi.
Adhadah yayi zaman kaso a shekarar 2012 bisa zargin ta'addanci.
Gwamnatin firai minista Nouri al-Maliki ta 'yan Shi'a ta sha zargin manyan 'yan siyasar kasar 'yan Sunni da alaka da kungiyoyin 'yan tawaye masu bore da makamai.