Mabiya addinin Krista kimanin dubu daya ne suka yi addu’a a birnin Yaounde, a kan nada Fasto Fonki Samuel a matsayin sabon shugaban kungiyar Majami'un Presby da kuma godewa Allah da sako mutanen yankin masu amfani da Ingilishi na ‘yan awaren Kamaru bayan mako guda da shugaba Paul Biya ya bada umarni ayi musu afuwa.
Mai magana da yawun mutane 120 da hukumomi suka sako su, Joseph Cho, ya ce suna rokon Biya ya sako shugabanninsu domin a zauna lafiya.
Ya ce muna da shugabanni, idan aka sako wadannan shugabannin namu za a samu sauki. Mutane kamar Sissiku da Mancho Bibixcy da aka kama saboda wannan batu. Mun dade muna tunanin za a sako su, inda kuwa an sako su da abubuwa basu tabarbare kamar yanda yake a yanzu ba.
Facebook Forum