Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yaki Da Cutar Ebola: Har Yanzu Akwai Sauran Aiki - WHO

Wasu ma'aikatan lafiya yayin da suka kai dauki a wani gida da aka samu wani da cutar Ebola a Congo
Wasu ma'aikatan lafiya yayin da suka kai dauki a wani gida da aka samu wani da cutar Ebola a Congo

Hukumar ta WHO, ta ce har yanzu, akwai sauran jan-aiki a gaba, amma ta ce wasu matakai da aka dauka, sun sa an samu nasara wajen dakile yaduwar cutar a yankunan Mangina, Beni, Komanda da Oichi.

Watanni shida bayan da aka ayyana barkewar cutar Ebola a Lardin Arewacin Kivu da ke Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta nuna alamun ana samun nasarar shawo kan bazuwar da cutar mai saurin kisa ke yi.

A kididdiga da hukumar ta WHO ta yi, ta ruwaito cewa adadin mutanen da suka kamu da cutar ya kai 752, inda daga cikinsu 465 suka rasa rayukansu.

Hukumar ta WHO, ta ce har yanzu, akwai sauran jan-aiki a gaba, amma ta ce wasu matakai da aka dauka, sun sa an samu nasara wajen dakile yaduwar cutar a yankunan Mangina, Beni, Komanda da Oichi.

"Lallai ina da kyakkyawan zato, na bayyana karara cewa, akwai bukatar mu ci gaba da aiki, ya zama dole mu tabbatar cewa, ba a samu koma-baya ba, a yankunan da muka samu nasara.” Inji Darektar hukumar ta WHO a yankin nahiyar Afrika, Matshidiso Moeti.

Ta kara da cewa daga cikin matakan da suka dauka, wadanda suka sa aka samu nasara, akwai horar da ma’aikatan lafiya, hada kai da al’umomin da lamarin ya shafa, da kuma bin diddigin duk inda aka samu bullar cutar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG