Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yaki da Cin Hanci da Rashawa A Jihar Neja Ya Shiga Rudani


Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello
Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello

Bisa ga alamu batun yaki da cin hanci da rashawa da almundagahana da gwamnatin jihar Neja tace tana yi tamkar ya gurgunce ko kuma yana barci ba'a san yadda za'a tadashi ba ya kama tafiya.

Batun ya shiga wani irin rudani da rashin sanin inda aka sa gaba, za'a yi yakin gadan gadan ne ko ba za'ayi ba.

Tun lokacin da aka rantsar da Alhaji Abubakar Sani Bello a matsayin gwamnan jihar ya lashi takobin dawo da makudan kudaden da aka ce an sace lokacin gwamnatin da suka gada tare ma da hukumta wadanda aka samu da laifin satar.

Daga bisani gwamnatin Alhaji Sani Bello ta samu nasarar bankado wata muguwar sata ta sama da Nera miliyan dari biyu da hamsin da daya a ma'aikatar fanshon jihar tare da samun ma'aikatan hukumar fanshon su talatin da laifi.

Kodayake kawo yanzu babu wani cikakken bayani na hukumta mutanen saidai a 'yan kwanakin nan bayanai sun nuna cewa gwamnatin jihar ta yafewa shida daga cikin mutane talatin da ake tuhuma da laifin sata acewar shugaban hukumar fanshon na yanzu Malam Usman Tulau.

Inji Usman Tulau mutane shida aka bashi umurnin ya rubuta abu a kansu kuma yayi hakan. Yace a cikin wani yanayi shugaban kasa ko gwamna na iya yiwa mutane ahuwa.

Amma hukumar dake kula da harkokin ma'aikatan jihar tace bata san da batun yafewa wasu su shida ba, inji kwamishanan hukumar Kwamred Adam Erana. Yace batun yafewa bai ma taso ba. Duk wanda yake da laifi sun riga sun yanke hukunci a kansa. Saboda haka babu daya da aka yafe masa.

Yanzu dai majalisar dokokin jihar tace tana bincike akan lamarin. Malik Madaki Boso shugaban kwamitin dake kula da harkokin ma'aikata na majalisar yace mutane talatin ne da ake tuhuma amma akwai wasu shida cikinsu da laifinsu ma yi muni an rubutawa gwamna wasika ya yafe masu.

Mustapha Nasiru Batsari nada karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG