Daya daga cikin manyan abubuwan dake ci wa jarumai Kannywood tuwo a kwarya shi ne yadda masoya kan tunkare su kai tsaye ba tare da kyakkyawan fuska ko gabatar musu da sallama a haduwarsu ta farko ba ,inji jarumi Ali Ibrahim wanda aka fi sani da Ali Dawaiyya.
Ali Dawaiyya ya bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir, a Kano, ya kara da cewa masoya basu li’akari da yanayi a lokaci da suka dunfari jarumi a haduwar su ta farko kwatsam sai su tunkarosu kamar da ma can sun dade da saninsu.
Ya ce mafi yawan lokuta masoya basu yi musu uzuri da zarar an sami rashin sa’a na rashin samun kyaukkyawan yanayi na karbansu ,sai su ce anyi musu girman kai tare da yi musu kudin goro na cewar ai ‘yan fim girman kai ne da su.
Ali Dawaiyya ya ce, ya fara harkar fim ne tun daga tushe inda ya faro daga mai rike hasken wuta har ya kai matsayin furodusa da kuma jarumi
Ya ce a mafi yawan lokuta ya fi fitowa a matsayin mara ji mai dabiu marasa dadi , duk a yunkurin fadakar da makomar ire-iren wadanda ke da wannan dabi’ar domin su farga su kuma canza.
Facebook Forum