Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda ‘Yan Kungiyar Lakurawa Suka Kashe ‘Yan sanda Biyu


Ofishin rundunar 'yan sanda a jihar Sokoto
Ofishin rundunar 'yan sanda a jihar Sokoto

A wata sanarwa da ta fitar, Rundunar 'yan sandan Najeriya ta hannun kakakinta a jihar Kebbi, SP Nafi'u Abubakar, ta tabbatar da aukuwar lamarin.

Tsokacin da masana ke yi kan cewa bullar 'yan ta'addan Lakurawa barazana ce ga sha'anin tsaro a yankin arewa maso yammacin Najeriya, na ci gaba da zama gaskiya, domin Lakurawan na ci gaba da haddabar jama'a.

Wannan na zuwa ne yayin wani hari da suka kai a jihar Kebbi a ranar Jumu'a inda suka kashe jami'an 'yan sanda biyu suka yi awon gaba da dabbobi masu tarin yawa.

'Yan ta'addan nan da ke zuwa daga kasashen ketare da ake kira da suna Lakurawa na ci gaba da haddabar mutanen yankunan da suke ziyarta duk da yake mahukunta na kan aikin shawo kan ayyukansu.

Bayan harin da suka kai a garin Mera na jihar Kebbi a watan Nuwamba na 2024, kwatsam sai ga wani hari sun sake kawowa wannan karon a garin Natsini da ke kan hanyar Argungu zuwa Kangiwa inda suka mamaye rugagen Fulani suka sace dabbobin jama'a masu tarin yawa.

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta hannun kakakin ta a jihar Kebbi, SP Nafi'u Abubakar, a wata sanarwa da ta fitar ta tabbatar da aukuwar lamarin sai dai ta ce jami'an sun kai daukin gaggawa suka yi musayar wuta da Lakurawan suka kore su, suka kuma kwato dabbobi masu yawa.

Sai dai kuma rundunar ta rasa jami'ai biyu a lokacin musayar wutar.

Daga cikin jami'an da suka rasu akwai Basiru Muhammad Kamba kamar yadda iyalansa suka tabbatarwa Muryar Amurka.

Tuni dai jama'a ke ci gaba da zaman zullumi a kan wannan hari da kuma ayyukan na Lakurawa.

Dama masana suna tsokaci a kan barazanar da ayyukan Lakurawan ke yi ga zaman lafiyar yankin Arewa Maso yammacin Najeriya da ma wasu kasashen Afirka, kamar yadda Dokta Murtala Ahmad Rufa'i na Jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto ke cewa.

Rundunar tsaron Najeriya dai ta sha fitowa tana bayyana azamarta wajen kawar da wadannan 'yan ta'addar na Lakurawa a wuraren da suke zama a yankin arewa maso yamma.

Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir daga Sokoto:

Yadda ‘Yan Kungiyar Lakurawa Suka Kashe ‘Yan sanda Biyu.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:07 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG