A bangaren laliga na kasar Spain 2016/2017 mako na 31 an fafata kamar haka kungiyar kwallon kafa ta Espanyol, ta doke Alaves, da ci 1-0 Real Madrid, tayi kunnen doki 1-1 tsakaninta da Atletico Madrid, Sevilla ta lallasa Deportivo, da kwallaye 4-2 Malaga, ta samu nasara akan Barcelona, da kwallo 2-0 Granada ta sha kashi a hannun Valencia, da kwallo 3-1 Celta Vigo 0 Eibar 2 Osasuna ta doke Leganes daci 2-1 Las Palmas ta sha Real Betis 4-1.
A yau kuma za'a buga wasa daya da ya rage tsakanin Real Sociedad, da Sporting da misalin karfe takwas saura kwata agogon Najeriya da Nijar.
Real Madrid ke Jan ragamar teburin da maki 72 sai Barcelona da maki 69 a matsayi na biyu Atletico Madrid a matsayi na ukku da maki 62.
Kasan teburin kuwa Sporting Gijon tana mataki na sha takwas da maki 22 Granada tana mataki na sha tara da maki 20 sai Osasuna a matsayi na ashirin da maki 17.
A wasannin da aka buga bangaren Firimiya lig na shekarar 2016/2017 mako na talatin da biyu a can kasar Ingila ranar Asabar, kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta lallasa Watford daci 4-0 Stoke City ta sha kashi a hannun Liverpool da kwallo 2-1 Manchester ta doke Hull City, da kwallaye 3-1 Middlesbrough's ta yi canjaras 0-0 tsakainta da Burnley Westham 1-0 Swansea Westbromwich 0-1 Southampton Itama kungiyar Bournemouth ta sha kashi a gidanta da ci 3-1 a hannun Chelsea
A jiya lahadi kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, ta bi Sunderland har gida ta lallasa ta da kwallaye 3-0 Everton ta doke Leicester City da kwallaye 4-2
A yau kuma za'a kara tsakanin Crystal Palace da Arsenal da misalin karfe takwas na dare agogon Najeriya Nijar kamaru da Chadi
A saman teburin na Firimiya, har yanzu Kungiyar Chelsea ke Jan ragamar teburin da maki 75, Tottenham tana mataki na biyu da maki 68 sai Liverpool a matsayi na uku da maki 63.
A kasan teburin kuwa Swansea, a mataki na goma sha takwas da maki 28
Middlesbrough's a mataki na goma sha tara da maki 24 ita kuma Sunderland ta mataki na ashirin da maki 20.
Ga Bala Branco da karin bayani.