Rahotanni da kuma shaidun gani da ido sun bayyana cewa cikin dare ne mayakan Boko Haram suka kai sabon farmaki inda suka yi yunkurin shiga garin Michika da kuma wasu yankuna na Madagali da ke kusa da dajin Sambisa.
Wannan sabon harin dai ya jefa al’ummar kananan hukumomin biyu da a baya suka taba fadawa hannun Boko Haram cikin fargaba na abin da ka iya faruwa.
Ko da yake, kawo yanzu hukumomin tsaro a jihar ba su yi karin haske ba kan wannan harin, to sai dai kuma shugaban karamar hukumar Madagali Hon. Aiden Tsukom Pallam wanda ya tabbatar da faruwan lamarin ya yaba da namijin kokarin da dakarun Najeriya suka yi wajen fatattakar mayakan na Boko Haram.
Shi dai wannan sabon harin na zuwa ne a kasa da kwanaki uku da ziyarar da babban hafsan askarawan Najeriya Lt.Janar Tukur Yusuf Burutai ya kai yankin Madagali.
Ya kai ziyarar ce don ganin halin da ake ciki inda ya bayyana irin matakan da ake dauka domin kawo karshen matsalar masu ta da kayar bayan.
A karshen makon da ya gabata ne, hukumomin kasar suka bayyana wnai shiri na janye dakaru daga yankin, matakin da wasu ke ganin akwai bukatar a sake tunani.
Ga dai Ibrahim Abdulaziz da cikakken rahoton:
Facebook Forum