Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Shugaba Issoufou, Bazoum, Ousmane Suka Kada Kuri’unsu


Mohamed Bazoum (Hoto: Fadar shugaban kasa)
Mohamed Bazoum (Hoto: Fadar shugaban kasa)

Da safiyar yau shugaba Issoufou Mahamadou na Jamhuriyar Nijar ya kada kuri’arsa a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa da ake yi a Nijar. 

Da misalin karfe 10:15 na safe ne Issoufou ya shiga harabar cibiyar zabe ta daya da ke kusa da fadar shugaban kasa a birnin Yamai, ya kada kuri’arsa tare da uwar gidansa.

A yayin wata ganawa da manema labarai bayan da ya kada kuri’a, Shugaba Issoufou ya yi kira ga ‘yan Nijar da su hada kansu a daina nuna bambanci.

Ya kuma yabawa jami’an hukumar zabe ta CENI da na tsaro wadanda suka jajirce wajen ganin zaben ya kankama.

Jim kadan bayan da shugaba Issoufou ya kada kuri’arsa, shi ma dan takarar jam’iyya mai mulki ta PNDS Tarayya Mohamed Bazoum, ya kada kuri’arsa a rumfar zaben da Issoufou ya kada.

“Na gamsu domin duk kurakuran da muka shaida a zaben da ya gabata yau sati biyu an yi musu gyara,” abinda Bazoum ya fada kenan a lokacin da aka tambaye shi ko ya gamsu da yadda zaben ke gudana.

A can Damagaram, shi ma dan takarar jam’iyyar RPR Canji, Mahamane Ousman, wanda ya taba mulkar kasar a baya, shi ma ya kada kuri’arsa da safiyar ranar Lahadi.

Ousmane shi ne dan takarar da ya samu goyon bayan magoya bayan jam’iyyar Lumana wacce ba ta da dan takarar shugaban kasa.

“Fatan da muke shi ne a yi wannan zabe lafiya. Sai dai ba za mu yarda da satar kuri'u ba, za mu bi hanyar da ta dace.” In ji Ousmane.

Rahotanni sun nuna cewa kusan daukacin zaben ya gudana ba tare da wata gagarumar tangarda ba.

XS
SM
MD
LG