Jami'an tsaron Najeriya sun tare daya daga cikin shugabanin Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Naejeriya ta CNG, Nastura Ashir Shariff bayan ya halarci zanga-zangar lumana da aka gudanar a Katsina.
Ashir yana daya daga cikin jiga-jigan da suka halarci zanga-zangar lumanar da aka yi a Katsina wanda daga nan ne jami'an tsaro suka tafi fa shi zuwa babban birnin tarayya Abuja kamar yadda mai magana da yawun CNG Suleiman Abdulzaeez ya tabbatarwa da Muryar Amurka.
A cewa Abdulazeez bayan zanga-zangar ne suka kai wa Kwamishinan 'yan sanda na Katsina gaisuwar ban-girma saboda goyon bayan da ya ba da a lokacin zanga-zangar wacce aka yi ta cikin lumana.
Daga nan sai aka ce Sufeto Janar na 'yan sanda Mohammed Adamu ya ce yana so ya gana da Nastura Ashir har ma ya aiko da mota a dauki shi Shariff din zuwa Abuja a cewar Abdulazeez.
Daga nan ne ya ce suka fahimci cewa akwai wani abu a kasa. Abdulazeez ya ce Jami'an tsaron na tuhumar Nastura Ashir da laifin zagin Femi Adeshina wanda shi ne mai magana da yawun Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Sai dai masana kundin tsarin mulkin Najeriya irinsu Barista Mainasara Kogo Ibrahim ya ce kundin tsarin mulki ya ba kowa 'yancin fadin albarkachin bakinsa matukar bai sa6a doka ba.
A cewarsa, doka ba ta amince da rike mutum fiye da sa'o'i 24 ba idan ba a gurfanar da shi a gaban kuliya ba.
Shi ma mai magana da yawun Kungiyar Dattawan Arewa Dr. Hakeem Baba Ahmed ya ce ya yi mamaki kwarai da tsare Nastura da hukuma ta yi domin su ba su ji ba, kuma ba su ga wani laifi da ya yi ba,.
Sai dai duk yunkurin da VOA ta yi na neman jin ta bakin 'yan sanda game da tsare Nastura abin ya cutura.
Saurara karin bayani a Sauti:
Facebook Forum