Mai magana da yawun gwamnan jahar Kaduna, Malam Samuel Aruwan ya ce gwamnati ta gano cewa hare-haren ramuwa ne ke mai da hannun agogo baya kan tsarin tsaro.
Inda ya yi kira ga dukkan mutanen da suke ganin an yi musu ba daidai ba, da su sanar da jami’an tsaro maimakon daukar hukunci a hannu.
To ko me rundunar yan-sandan jahar Kaduna ke yi don shawo kan hauhawar hare-hare a jahar? DSP Yakubu Sabo, mai magana da yawun rundunar yan-sandan jahar ta Kaduna ya ce a kullum runudanar ‘yan sandan na kira ga al’umomin yankin Kajuru, akan su taimaka wajen baiwa jami’an tsaro hadin kai da bayanai akan dukkan wani ko rukunin mutanen da ba a yarda da su ba. A kuma guji daukar doka a hannu.
Shi kuwa shugaban kungiyar Miyatti Allah na karamar hukumar Kajuru, Ardo Musa Aliyu, cewa ya yi su ba sa ramako amma akwai bukatar gwamnati ta rinka hukunta masu laifi.
Ya zuwa yanzu dai an dan sami natsuwa a yankin Kajurun Jahar Kaduna tun bayan harin safiyar litinin da ya yi sanadiyar kashe mutane 21 da sace shanu hamsin da kuma kona gidaje 10.
Domin karin bayani saurari rahotan Isah Lawal Ikara.
Facebook Forum