Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Aka Yi Bikin Ranar Ma'aikata a Nijar


Sallar ma'aikata a Jamhuriyar Nijar inda kungiyar malaman makarantu ke sanye da bakaken kaya domin nuna bakin cikinsu bisa ga halin da ilimi yake a kasar
Sallar ma'aikata a Jamhuriyar Nijar inda kungiyar malaman makarantu ke sanye da bakaken kaya domin nuna bakin cikinsu bisa ga halin da ilimi yake a kasar

Ranar daya ga watan Mayu na kowace shekara ne ake bikin tunawa da ma'aikata a duk fadin duniya a Jamhuriyar Nijar ma ba'a bar ma'aikata a baya ba

Ma'aikatan a karkashin jagorancin kungiyoyinsu sun fito inda suka gudanar da jerin gwano daya bayan daya a gaban gwamnonin jihohi da jama'a kamar yadda aka saba kowace shekara domin mika kokensu..

Mamman Galadima shugaban uwar kungiyar kwadago ta kasa reshen Damagaran ya bayyana yadda sallar ta zo masu. Yace abubuwan da suka damesu akan makarantun kasar ne suka fito su fada saboda duk lokacin da mutum bashi da 'ya'ya masu ilimi to ya shiga halin kakanikayi. Yace su sun kare a jahilai idan kuma 'ya'yansu sunkare a jahilai sun lalace kuma kasar ma ta lalace.

Ya cigaba da cewa harkar ilimi a kasar ya kama hanyar mutuwa lamarin da ya zama masu abun takaici. Abun da kuma yake ci masu tuwo a kawarya shi ne rashin daukan matasa aiki cikin shekaru biyu da suka wuce a duk fadin kasa. Lamari ne da dole a dubashi.

Tambai Musa jagoran wata kungiyar ta ma'aikata ya kira a duba matsalolin ma'aikata musamman harkar ilimi. Yace ja-in;ja dake tsakanin malaman makarantu da mahukumta bai dace ba. Suna son a samu a daidaita. Su zauna teburin shawara domin a samu masalaha.

Malaman kuma da suka fito cikin bakaken kaya sun nuna takaicinsu na halin ko inkula da mahukumta ke nuna masu, inji Malam Yau Abdu magatakardan kungiyarsu.Bakaken kayan da suka sa suna nuna wa duniya irin bakin cikin da suke ciki ne. Gwamnati a kowane mataki tana yiwa ilimi rikon sakainar kashi, inji Yau Abdu.

Shi kuwa gwamnan jihar Damagaran Isa Musa bayan barka da salla da yayi masu ya karbi koken ma'aikatan tare da cewa zasu zauna kan teburin tattaunawa.

Ga rahoton Tamar Abari da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG