WASHINGTON, DC —
A yau jumma’a aka fito da jadawalin yadda za a gwabza a wasannin kwata-fainal na cin kofin zakarun kulob-kulob na Turai, inda ake ganin za a yi karon batta ba kadan ba.
A daya daga cikin wasannin na kwata-fainal, Atletico Madrid da FC Barcelona, dukkansu masu hankoron lashe wasannin lig-lig na kasar Spain, zasu kece raini, yayin da daya kungiyar ta kasar Spain, Real Madrid zata gwabza da Borussia Dortmund (domin ta yi kokarin rama kashin da ta sha a hannun Dortmund a wasan kusa da karshe bara).
Su kuma kungiyoyi biyu na kasar Ingila da suka rage, zasu fuskanci manyan abokan adawa, inda Chelsea zata yi arangama da zakarun kasar Faransa, Paris Saint Germain, ita kuma Manchester United zata kara da zakarun kulob kulob na Turai na yanzu, watau Bayern Munich.
Za a yi karawar farko a tsakanin kungiyoyin a ranakun 1-2 ga Afrilu, sai kuma a yi karawa ta biyu a ranakun 8-9 Afrilu.