Wani fitattacen jigo a masana’antar shirya fina-finan Hausa, Hafizu Bello ya ja hankalin hukumomi da masu ruwa da tsaki na masana’antar Kannywood da su duba yiwuwar tsaftace fina-finai da ake fitar da su domin gidajen talabijin da kafofin sadarwa gudun fitar da dabi’un da basu dace ba ga al’umma.
Ya bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da wakiliyar DandalinVOA, Hafizu Bello wanda ya shafe kimanin shekaru ashirin a masana’antar Kannywood ya ce, samun cigaban fitar da fina-finai a kafar sadarwa na cike da kalubale da dama muddin ba’a samar da wata doka da zata rika duba ire-iren fina-finan da ake fitarwa ba domin wannan kafar.
Ya kara da cewar masana’antar Kannywood ta samu cigaba da dama ciki harda samar da hanyoyin dakile masu satar fasaha ta hanyar daina fitar da fina-finai a faifan bidiyo ko CD ga mafi yawa masu harkar fim.
Wannan kuwa ya biyo bayan cigaban zamani da amfani da gidajen talabijin da kafofin sadarwa don magance matsalar satar fasaha.
Facebook Forum