Sheikh Gumi yace a kowace kusurwa ta duniya, Musulmi da kasashen Musulmi su na karbar wannan rigakafi hannu bibbiyu domin su raba 'ya'yansu da cutar mai gurgunta wadda ta kama, a yayin da Hausawa da Fulani kadai a Najeriya suke nuna turjiya.
Yace ko a cikin Najeriya, yankunan kudancin kasar su na karbar wannan rigakafi hannu bibbiyu, kuma a arewacin Najeriya din ma, sauran kabilu su na karba, sai Hausawa da Fulanin kadai ke nuna kyamar wannan maganin mai matukar amfani.
Yace Musulunci bai haramta maganin rigakafi ba, kuma akasarin manyan malaman addinin Musulunci a fadin duniya sun hadu sun yi ittifaki da cewa karbar maganin rigakafin cutar shan inna ta Polio yana da amfani kuma ya kamata a yi shi.
Yace dukkan manyan kasashen Musulmin duniya kamar su Saudi Arabiya, Masar, Indonesiya, da kasashen arewacin Afirka na Musulmi duk su na karbar wannan maganin.
Ya shawarci Hausawa da Fulani da su rungumi wannan maganin.