Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Xi Jinping Zai Dauki Mataki Akan Hare-hare


Shugaban Chana, Xi Jinping.
Shugaban Chana, Xi Jinping.

​Shugaban China Xi Jinping ya sha alwashin daukar kwararan matakai bayan wasu munana hare haren bom da wakake da aka kai a wata tashar jirgin kasa a lardin Xinjiang da ke yammacin kasar.

Jami'ai sun ce an hallaka mutane uku an kuma raunata mutane 79 da yammacin jiya Laraba bayan da maharan su ka tayar da bama-bamai tare da taba ma fasinjoji wukake a tashar kudu ta hedikwatar yankin.

Jaridar gwamnati mai fitowa duk rana ta fadi yau Alhamis cewa cikin mutane ukun da aka kashe har da wani wanda ke tsaye da kuma biyu daga cikin maharan, koda yake rahoton bai bayyana dalla-dalla ko harin kunar bakin wake ba ne.

Kafar yada labaran gwamnatin China, Xinhua, ta ce mutane biyun da ake zargi sun jima su na aikata abubuwa na tsattsauran ra'ayin addini.

An sake bude tashar jirgin kasar cikin tsauraran matakan tsaro.

An kai harin ne a ranar da Mr. Xi ya kai ziyara a Xinjiang, inda ya sha alwashin daukar tsauraran matakai kan wadanda gwamnati ta kira 'yan aware.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG