Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wutar Daji Ta Lakume Rayuka Da Asara a Yankin Tekun Mediterranean


A Firefighter in the line of duty.
A Firefighter in the line of duty.

Yayin da ake fama da matsanancin zafin ranar bazara, wutar dajin dake ci a yankin Meditrranean ya janyo asarar rayuka da dukiyoyi.

Yanayin muhalli a yankuna kasashen dake kusa da tekun Mediterranean sun kara dumama sossai yayin da ake fama da matsanancin zafin ranan bazara mai tsanani a jiya Talata kana ‘yan kwana-kwana suna ta kokarin kashe wutar dajin da take ci a fadin yankin.

Akalla mutane 34 ne suka mutu a Algeriya. A Croatiya kuma, water dajin dake ci ta karasu akalla km 12 kusa da garin Dubrovik a yammacin jiya Talata.

Musamman Girka ne yanayin yafi Kamari inda hukumomi suke kokarin kwashe sama da mutane dubu dari biyu (200,000) daga gidajensu da kuma wuraren hutawa dake kudancin tsibirin hutawa na Rhodes cikin ‘yan kwanakin da suka gabata.

Bisa alkaluman ma’aikatar siffiri, kimanin ‘yan yawon bude ido dubu uku (3,000) ne suka koma kasashen su cikin jirgin sama a jiya Talata kana masu kamfanonin yawon bude ido sun soke tafiye-tafiyen da suka shirya nan gaba.

Matuka jiragen sama biyu masu feshin ruwa sun mutu bayan da suka rutsa duwatsu a tsaunuka kusa da garin Karystos a tsibirin Evia dake gabashin Athens.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG