WASHINGTON, DC: —
Mai horar da 'yan wasan kungiyar Kwallon kafa ta Leicester City Brendan Rodgers, ya bayyana cewa dan wasan tsakiyar kungiyar dan asalin Najeriya, Wilfred Ndidi, ya murmure daga tiyatar da aka yi masa.
Ndidi ya samu rauni a sansanin atisaye, yayin da kungiyar ke shirye-shiryen fafatawa da Southampton, wanda ta yi nasara da ci 2-1 a gasar Premier League na bana.
Kungiyar Kwallon kafa ta Leicester City dai a yauzu haka ita ke mataki na biyu a teburin gasar na bana, a wasanni mako na 23 inda take gaban Manchester City.
Sai dai Rodgers bai bayyana ranar da dan wasan tsakiyar zai dawo filin wasa ba.
Facebook Forum