Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wayar Wutar Lantarki Ta Hallaka Masoya Kwallon Kafa 30


Rahotanni sun bayyana cewa a kalla mutane talatinne suka rasa rayukansu a yayin da suke kallon kwallo a Calabar, babban birinin jihar Cross River, sakamakon tsinkewar wata wayar wutar lantarki data gitta ta saman gidan da suke kallon kwallon.

A cewar rahotanni daga gidan Talabijin na channels, wayar wutar ta tsinke ta kuma fada a kan dakin da mutanen suke kallon wasan wanda ake fafatawa tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Manchester auanited da Anderleht.

A cewar wani da ya sami kubuta daga gidan, ya bayyanawa gidan Talabijin din cewar wayar ta tsinke kuma ta fada kan kwanon gidan, lamarin da ya haifar da tashin wuta.

Ma'aiktar wutar lantarki ta Najeriya ta ce ba a kan ka'ida aka gina gidan ba, domin kuwav layin an kebe shi ne domin babbar wayar da ke tura wuta tsakanin jihohi wato High tension cables.

Saurari cikakken bayanin a nan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG