Ministan yace amma a wannan karon ba zamu sake bari duniya ta barmu a baya ba a watan Yunin wannan shekarar lokacin da kasar zata koma kan kimiyar zamani.
Dalili ke nan da aka kafa kwamiti a karkashin minista dake zama akai akai domin cimma wannan nasarar. Ministan yada labarun Najeriya Lai Muhammad shi ya yiwa manema labaru bayani akan barin hanyar gargajiya zuwa ta kimiyar zamani, kafar da kasashen da suka cigaba ta fuskar sadarwa suka koma tuntuni.
Wannan sabuwar fasahar hukumar kula da gidajen rediyo da talibijan ta Najeriya ko NBC ta fasara a Hausa da kaura daga sadarwa ta mai dungu wato analogue zuwa mai yatsu wato digital da kuma ake yadawa a Najeriya tun bara da aka kammala shirin a Jos.
Wannan sabuwar fasaha ana iya hada akwatunan talibijan talatin wuri daya da mutane ka iya kallon tasoshin kyauta.
Zuwa yanzu dai Jos da Abuja ke kallon wannan naurar ta NBC.
Lai Muhammad yace duk da kalubale da cikas ake fuskanta akwai bukatar dagewa wajen cimma wannan muradun a watan Yunin wannan shekarar.
Tsohon shugaban NBC Danladi Bako yayi karin bayani. Yace idan mutum nada akwatin yana iya kallon tasoshi talatin daga koina a kasar. Yace duk wasu gidajen rediyo da talibijan ana hadasu layi guda sai a watsasu. Haka kuma duk wani abun da bai kamata ba wannan layin zai tosheshi.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Facebook Forum