Kamfanin Facebook ya ce ya cire wasu daruruwan shafukan bogi, saboda yadda aka yi amfani da wata fasahar zamani da ke kirkirar fuskokin mutane na bogi, kuma ta na amfani da su a shafin FaceBook don ma’abota shafin da shi kansa kamfanin na Facebook.
Masu amfani da shafin kan zaci mutanen gaske ne, a cewar kamfanin sada zumuncin zamani. Kwararrun da su ka yi nazarin shafukan sun ce wannan ne karon farko da suka taba ganin an yi amfani da fuskoki na bogi sosai a matsayin wata hanyar isar da sakonni ta kafar sada zumuncin.
Wadannan shafukan da kamfanin Facebook ya cire a ranar Jumma’ar da ta gabata, na zaman wani bangaren wani dandalin yada labarai, wanda yawancin lokuta ke sanya abubuwan nuna goyon bayan shugaba Donald Trump, da nuna adawa da gwamnatin China, a cewar kwararrun da suka duba shafukan.
Yawancin kafofin sun yada abubuwa akan Facebook da wani shafin yanar gizo da ake kira The BL. Kamfanin Facebook ya ce shafukan na da alaka da wani kamfanin yada labarai, da ake kira Epoch Media Group na Amurka, wanda ke da jaridar Epoch Times, jaridar da ke da alaka da ‘yan gwagwarmayar Falun Gong da ke muradin gwamnatin Trump.
Ko da yake mai wallafa jaridar ta Epoch Times ya musanta zargin cewa kamfaninsu na da wata alaka da BL.
Facebook Forum