Wata matashiya ‘yar shekaru 16 da haihuwa, ‘yar gwagwarmayar kare yanayi daga kasar Sweden ta tsallaka tekun Atlantika da wani karamin jirgin ruwan wanda kwata-kwata bai fitar da iskar gas (mara kyau) ba don ta halarci wani babban taron kasashen duniya akan dumamar yanayi.
Greta Thunberg, da sauran abokan tafiyarta sun fuskanci gargada akan teku a lokacin da suke kan hanyar su ta zuwa birnin New York. Makonni biyu suka kwashe su na wannan tafiyar.
Matashiyar ta ki yarda ta shiga jirgin sama don ta taimaka wajen kawar da irin gurbatacciyar iskar da jirgin sama ke fitarwa. "Daukar mataki akan sauyin yanayi" shi ne taken zanga-zanagar da ta sha jagoranta a Sweden, abinda ya janyo yajin aikin dalibai a kusan birane 100 a fadin duniya.
Ana sa ran Greta zata yi jawabi a wani taron kolin Majalisar Dinkin Duniya da za a yi game da sauyin yanayi wata mai zuwa.
Facebook Forum