Wata kotun daukaka kara a kasar Brazil ta bada umarnin a ci gaba da garkame tsohon shugaban kasar Luiz Inacio Lula Da Silva a gidan yari, ta canja hukuncin da wani alhaki a wannan kotun ya yanke, tunda farko a jiya Lahadi cewa a saki tsohon shugaban.
Alkali Sergio Moro wanda shine ya yanke hukuncin daurin da aka yiwa tsohon shugaban a watan Afrilu bisa samunsa da laifin ci hanci da rashawa, yace kotun daukaka karan bata da ikon sakin tsohon shugaban, dan siyasa mai farin jinni a kasar sosai.
Duk da hukuncin daurin shekaru goma sha biyu da aka yanke masa a bara, tsohon shugaba Lula yana da farin jinni a kasar. Kdiddiga da aka yi ya nuna cewa, idan tsohon shugaban ya sake tsayawa takara, zai iya lashe zabe a karo na uku a zaben da za’a yi a watan Oktoba.
Ya ja ragamar mulkin Brazil daga shekara ta dubu biyu da uku zuwa shekara ta dubu biyu da goma sha daya.
Facebook Forum