'Yar wasan tseren kasar Afrika ta Kudu mai suna Caster Semenya, bata samu nasara a kotu ba, na daukaka karar da ta yi kan wasu sabbin dokokin da hukumar da ke kula da 'yan wasan motsa jiki ta duniya (IAAF) ta kawo kan rage kuzarin halittar maza da ake iya samu a jikin mata masu kirar maza da ke wasan tsere.
Kotun da ke sauraren kararrakin harkokin da suka shafi wasanni ta yi watsi da karar da Caster Semenya, ta shigar a gabanta, inda ta kalubalanci sabbin dokokin na hukumar ta IAAF.
Kotun na nufi cewar yanzu ita da sauran takwarorinta masu irin wannan halittar nata, dole su rika amfani da shan maganin da zai rika rage musu kwayoyin halittar maza, kafin su samu damar shiga gasar tseren mita 400, da kuma sauran wasanni ko kuma su sauya wasa.
Sai dai kotun ta ce ta damu dangane da yadda za a rika amfani da wadannan sabbin dokokin a nan gaba.
'Yar wasan Semenya mai shekara 28, da haihuwa tana da halitta na mata da maza, tace waddannan sabbin dokokin ba ayi adalci ba, inda ta ce tana so ne ta rika yin wasan tserenta kamar yadda aka halicce ta.
'Yar wasan dai a shekarun baya ta fafata a wasanni daban daban na maza dana mata, sai dai daga baya hukumar kula da wasannin ta bayyana cewa, dole sai dai ta zabi jinsi daya ko mace ko kuma namiji, idan tana son ta cigaba da fafata wasannin, bayan haka kuma duk kyaututtukar data samu zata mayar da su.
A shekarar 2009 ita ta lashe kambun Duniya na tsere wanda akayi a Berlin, haka kuma sau biyu tana lashe lambar yabo na gudun mita 800, a gasar motsa jiki na Duniya Olympic.
Facebook Forum