Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Ba'amurkiya da Mijinta da Aka Kubutar Sun Ki Shiga Jirgin Amurka


Mutanen da 'yan Taliban suka sace shekaru biyar da suka gabata kafin a kubutar dasu jiya Alhamis a Pakistan
Mutanen da 'yan Taliban suka sace shekaru biyar da suka gabata kafin a kubutar dasu jiya Alhamis a Pakistan

Ba'amurkiyar da mijinta dan asalin Canada da 'yan Taliban suka yi garkuwa dasu na tsawon shekaru biyar sun samu 'yanci jya Alhamis amma sun ki shiga jirgin da Amurka ta aika ya daukesu zuwa Jamus

Wata Ba’amurkiya da mijinta dan Canada da ‘ya’yansu uku na ci gaba da zama a kasar Pakistan ya zuwa daren jiya Alhamis, inda suke shirin dawowa gida, bayan shekaru biyar da suka kwashe a hannun mayakan Taliban da suka yi garkuwa da su.

Masana bayanan sirrin Amurka ne suka kyankyasawa dakarun Pakistan inda ake rike da mutanen, sannan daga baya aka je aka kubutar da Caitlan Coleman da mijinta, Joshua Boyle dan asalin Canada, a yankin kabilar Kurram da ke kusa da kan iyakar kasar da Afghnistan a ranar Larabar da ta gabata.

Wani jirgin saman Amurka ya jira ma’auratan da ‘ya’yansu bayan da aka kubutar da su domin ya kai su kasar Jamus inda za a duba lafiyarsu, to amma saboda wasu dalilai da ba'a tantance ba, Boyle ya ki hawa jirgin.

Coleman da mijinta, sun bata ne a shekarar 2012 yayin da suke yawon hawa tsaunuka a Afghanistan, inda daga baya kungiyar Taliban reshen Afghanistan ta dauki alhakin sace su.

Shugaban Amurka Donald Trump, ya yaba da sako su da aka yi, yana mai cewa hakan wata alama ce da ke nuna kyautatuwar dangantakar Amurka da Pakistan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG