Wasu 'yanbindiga da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne sun yiwa wasu yankan rago a garin Midul dake cikin karamar hukumar Madagali a jihar Adamawa Arewa maso gabashin Najeriya.
Rahotanni na cewa 'yan bindiga sun yi shigan burtu ne cikin dare inda suka farma kauyen mai tazaran kilomita ko zuwa bakwai zuwa garin Madagali inda suka yiwa wasu yankan rago yayinda aka garzaya da wasu asibiti sakamakon raunuka da suka samu.
Wani mazaunin garin yace 'yan ta'adan sun kama yanka mutane tare da harbi da bindiga baya ga kona gidaje da shagunan da suka yi.
Ko da yake kawo yanzu,hukumomin tsaro basu yi karin haske ba,to amma shugaban karamar hukumar Madagalin Yusuf Muhammad ya tabbatar da faruwan lamarin.
Shima dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Michika da Madagali Adamu Kamale ya bayyana tashin hankalin da suke ciki a yanzu.
Kawo yanzu tuni gwamnatin jihar ta saba layar taimakawa wadanda suka jikkata sanadiyar wannan hari. Ahmad Sajo dake zama kwamishinan yada labaran jihar ya bayyana cewa sojoji da kuma yan sakai na maharba sun sami kai dauki tare da kashe daya daga cikin yan ta’addan.
Wannan sabon harin dai na zuwa ne yayin da ake kammala wani taron sanin makaman aiki ga askarawan Najeriyan a Yola,batun da masana ke ganin akwai bukatar hada hannu.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.
Facebook Forum