Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'Yan Najeriya Sun Agazawa Ingila Ta Lashe Kofin Duniya


Kungiyar kwallon kafar Ingila na 'yan U-20
Kungiyar kwallon kafar Ingila na 'yan U-20

Tsohon dan kwallon Ingila Danny Mills, ya bukaci wasu matasa ‘yan asalin Najeriya, wadanda suka bugawa kasar Ingila tamola a gasar kwallon matasa na ‘yan kasa da shekaru ashiri watau U-20, wadanda kuma suka taka rawar ganin da ta baiwa Ingila nasarar lashe gasar da suyi waste da batun bugawa Najeriya tamola.

Matasan ‘yan Najeriya da suka bugawa Ingila wasan su shida, sun hada da Dominic Solanke, wanda kuma shi ya lashe kambin dan wasan da yafi fice a gasar da kuma Ademola Lookman. Sauran sun hada da Josh Onomah, Fikayo Tomori, Seyi Ojo da Ovie Ejaria.

Danny Mills, ya furta haka ne a wani shirin BBC, a daidai lokacin da ake buga wasan karshe tsakanin kasashen Ingila da Venezuela, ya kuma kara da cewa bari yayi son zuciya inda ya ce idan mutun ya sami damar bugawa Ingila wasa ya kamata ya rugumeshi.

Yace idan mutun yana Afirka yana iya zuwa gasar cin kofin kasashen Afirka, amma samun yin fice a faggen wasan kwallon kafa wasan kwallon a kasar Ingila yafi na Najeriya nesa ba kusa ba domin akwai damar buga wasani a gasar daban daban a Turai.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG