Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Mutane A jihar Niger Basu Gamsu Da Ayyukan Hukumar Zabe Ba


zaben Nijar a Najeriya
zaben Nijar a Najeriya

Hukumar Zabe mai zaman kanta na Nigeria tace tayi wa mutane dubu casain rajista a jihar Niger

Hukumar zaben Nigeria mai zaman kanta a jihar Niger tace mutane dayawan su yakai dubu casain da hudu tayi wa rajista a jihar.

Sai dai wasu yan jihar sun bayyana rashin gamsuwar su da wannan adadin dama yadda hukumar ke tafiyar da ayyukanta.

Mai Magana da yawun huumar a jihar ta Niger Mohammed Madawaki Wase ya jaddada wannan adadin kuma yace an kara samar da wasu wurraren karban wadannan katin zaben.

Sai dai wasu jamaa a jihar sunce zasu ci gaba da yiwa jamaar su yekuwa domin su fito su karbi wannam katin, kuma sun bukaci hukumar data kara samar da cibiyoyin karban wadannan katin zabe.

Shugaban Karamar hukumar Mariga Abdulmalik Sarkin Daji ya shaidawa Mustafa Nasir Batsari cewa duk da yake suna fadakar da mutane muhimmacin karban katin zaben amma wuraren karban su yayi karanci.

Ga Mustafa Nasir Batsari da karin bayani.3’10

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG