Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Mahara Sun Kashe Wani a Nijar


Hoton wani harin da aka taba kai wa a jihar Zamfara.
Hoton wani harin da aka taba kai wa a jihar Zamfara.

Al'ummomin birnin Konni na Jamhuriyar Njiar sun kwana cikin tsoro da zullumi bayan da wadansu mutane dauke da bindigogi suka yi harbe-harbe har suka kashe mutum daya, yayin da mutum biyar suka samu raunuka.

Garin na Konni da ke kan iyaka da Najeriya, ya shiga wani yanayi na dar-dar bayan da mutanen, wadanda ba a san ko su waye ba, suka yi ta harbe-harbe a daren jiya.

Maharan sun kuma kwashe kudaden ‘yan canji.

A yanzu dai jami’an tsaro na can na nemansu ruwa a jallo.

Daya daga cikin wadanda suka samu raunukan na cikin mawuyacin hali, amma tun cikin daren jiya aka kai su asibitin kauyen Galmi.

Wani da ya shaida lamarin kuma ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana wa wakilinmu Harouna Mamane Bako yadda lamarin ya faru.

Ya ce, “Abin da ya faru abu ne da bamu taba gani ba, da wajen karfe tara na dare wani yaro ya zo da bindiga, daga bisani ‘yan uwansa suka zo suma aka dinga harbe-harbe. Suka kuma kwashe kudaden ‘yan canjin da ke zaune a wurin.”

Hukumomi na bariki da na gargajiya na birnin, duk ba su yi barci ba, inda ma sai da jami’an tsaro suka tunkari wadansu matasa da suka so suyi bori cikin dare domin nuna rashin jin dadinsu game da abinda ya wakana.

Daga bisani dai an samu fatattakarsu.

Kasar ta Jamhuriyar Njiar na yawan fuskantar hare-hare cikin kwannakin nan.

Saurari cikakken rahoton a sauti daga bakin wakilinmu Harouna Mamane Bako.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00


Facebook Forum

Zaben 2023

TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Tasirin Da Zaben Donald Trump Zai Yi A Harkokin Kasashen Duniya.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:50 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG