Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Jami'an Gwamnati Suka Hana Sulhu da Kungiya Boko Haram


SHAIKH DAHIRU BAUCHI
SHAIKH DAHIRU BAUCHI

A cikin firar da yayi da Muryar Amurka Shaikh Dahiru Bauchi ya bayyana irin kokarin da yayi na kawo sulhu tsakanin gwamnatin Najeriya da kungiyar Boko Haram amma wasu jami'an gwamnati suka sa kafafu suka shure shirin

Kimanin shekaru biyu da rabi da suka wuce kungiyar Boko Haram ta amince ta yi sulhu da gwamnati idan shi Shaikh Dahiru Bauchi ya yadda ya shiga tsakani.

Kungiyar tace ta san shi ba zai yaudareta ba kamar yadda wasu suka yi masu kuma sun san gwamnati ba zata yaudareshi ba. Dalili ke nan ya shiga maganar yana zaton da gaske ne. A lokacin, bangaren Boko Haram da gaske suke yi.

Kungiyar tace idan gwamnati zata bada takarda a rubuce zata yadda. Ya ko gayawa gwamnati wadda ta bayar da takarda a rubuce. Bayan ya ba kungiyar takardar an yi kamar wata hudu ba'a yi wani abu ba. An daidaita cewa gwamnati ba zata kama 'yan kungiyar ba su kuma ba zasu kai hari ba har sai an kammala batun sulhu.

Amma abun mamaki cikin gwamnatin akwai wadanda basa son a yi sulhu kuma suna da karfi. Da kungiyar Boko Haram ta gane wannan sai ta ja da baya. Wadanda basa son a yi sulhun sai suka shiga cikin maganar suka lalatata. Sai shirin ya tabarbare. Hana sulhun nada riba a wurinsu wadanda suka hana a yi sulhun. Dalili ke nan kungiyar Boko Haram ta daina magana da shi.

Shaikh Dahiru Bauchi ya sha faman neman ya gana da shugaban kasa ta wajen mataimakinsa. Yayi har wajen sau goma. Amma da ya samu ya gana da shugaban kasan lokacin da ya nemesu ba'a ambato batun Boko Haram ba. Ba'a kuma nemi Shaikh din ba da wata magana sai daia an ce yayi addu'a kuma yayi.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:38 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG