Wasu 'yan jam'iyyar PDP da aka ci zarafinsu bayan zaben shakarar 2011 sun koka da rashin kulawa dasu da kuma rashin biyansu diya.
Bayan sakamakon zaben tashin hankali ya barke wanda yayi sanadiyar mutuwar wasu da kuma asarar dukiyoyi masu dimbin yawa a jihar Filato.
Magoya bayan jam'iyyar PDP a karamar hukumar Jos ta Arewa sun bayyana irin azabar da suka sha da matsalolin da suke fuskanta. Bayan zaben wasu tsageru sai suka dinga binsu gida gida suna gana masu azaba tare da kona gidajensu.
Alhaji Danladi Pashi yace da aka yi zabe aka bayyana sunan Jonathan a matsayin wanda ya ci sai wasu suka farmasu, suka kona gidajensu tare da dukiyoyinsu. Gwamnatin Filato ta sasu a otel na wajen wata bakwai kafin a fitar dasu. Gwamnatin tayi masu alkawarin taimakansu amma bata yi ba banda nera dubu ashirin ashirin da ta basu.
Hajiya Salamatu Ahmad tace tana cikin wadanda suka sha dan karen duka a unguwar Rogo har ma ana zaton ta mutu. Tayi wata biyu a kwance a asibiti tana jinya.
Babu wani kwamitin da basu je ba domin neman hakinsu. Wai sun rasa gidajensu kuma babu inda zasu sa kai idan an yi ruwan sama. Suna son a biyasu kamar yadda aka biya na koina inda rikicin ya rutsa dasu a wasu jihohi. 'Ya'yansu basa makaranta babu inda zasu sa kansu. Daga bisani wata ma barkewa tayi da kuka.
To amma kwamishanan labaran jihar Filato Alhaji Abubakar Muhammad Badu yace gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamitin nazari akan lamarin. Sabili da haka zasu jira sai gwamnatin tarayya din ta gaya masu abun da zasu yi. Ahalinda ake ciki ba zasu yiwa gwamnatin tarayya katsa landan ba.
Ga rahoton Zainab Babaji.