Wani furfesan jami’a y ace duk wata jam’iyya a Nijeriya wace ta ce ta na so ta kawo cigaban Nijeriya amma ba ta yi wani abu ba na a zo a gani a fannin rayuwar mutane kamar iliminsu da lafiyarsu da sauransu - wadanda su ke kawo cigaba ba – to abin takaici ne. Y ace muddun aka kyautata rayuwar mutane to kasa za ta samu cigaba sosai. Y ace muddun akasarin mutanen kasa ba a inganta rayuwarsu, saidai kawai a je a kawo kamfanonin kasashen waje su yi harkar mai, idan kuma an sayar a raba ma jihohi, kuma jihohin su kasa yin komai, babu inda za a je.
Furfesa Samuel Zalanga, wanda abokiyar aikinmu Grace Alheri Abdu ta zanta da shi, y ace koda yak e an sami ‘yanci fiye da shekaru 50 da su ka gabata an kasa samun cigaba saboda an kasa inganta rayuwar ‘yan kasa wanda shi ne kan gaba. Y ace kuma idan jam’iyyar siyasa za ta kawo cigaba ga al’umma to kar ta nuna banbancin addini ko na siyasa ko na kabila ko na jinsi.
Y ace yadda su kuma talakawa za su taka rawa wajen kawo cigabansu shi ne ta hada kawunansu don a sami zaman lafiya da kwanciyar hankalin da ake bukata. Y ace kodayake akwai banbancin addini da na kabila da na siyasa tsakanin jama’a, dole ne dai jama’a su hada kawunansu kafin hukuma ta sami cikakken sukunin kawo cigaba.