Yayin baje kolin fasahar duniya da aka gudanar a birnin Las Vegas ta kasar Amurka, wani mutummutumi ne ya dauke hankalin akasarin mahalarta taron. Mutummutumin da aka inganta shi da abubuwan ban al’ajabi.
A karon farko da aka kirkiro mutummutumi mai magana, ya yi tafiya kamar mutum, kana ya na aikin bada abinci ko abin sha, kai hasali ma yana buga kwallon tebur da aka fi sani da ‘Table Tennis.’
Akasarin na’urorin mutummutumin Robots da mutane kan saya su na da tsada, kuma ba kasafai su ke aiki kamar yadda aka ce ba, amma wannan babu abu daya da aka ce yana yi da ba za a ganshi ba.
Bilal Zuberi, wani mai bibiyar na'urori da yanayin aikin mutummutumi, ya ce ba za mu taba barin mafarkin mu na inganta nau’rar robot ba, domin kuwa ta haka ne kawai za a iya samun cigaba na wannan zamanin.
Ana iya cewa babu wani aiki a wannan karnin na 21, da za a ce naurar robot ba za ta iya aiwatar da shi ba cikin lokaci da inganci ba, don haka za a cigaba da ganin abubuwan al’ajabi da wadannan na’urorin zamanin.
Facebook Forum