Mai taimakawa gwamnan Borno kan labaru Isa Gusau yace faifan sauti da aka yada a yanar gizo dake nuna muryar gwamna Kashim Shettima ce da gwamna Ibikunle Amosun na Ogun inda suka caccaji 'yan kabilar Igbo ba gaskiya ba ne.
Isa Gusau yace wani mai neman takarar shugabancin Najeriya ne daga yankin arewa ya tsara sautin da zummar bata gwamna Shettima a yankin kudancin Najeriya.
Inji Isa Gusau sun san mutumin amma yanzu ba zasu bayyana sunansa ba har sai shekara ta 2019. Amma yace gwamnan Borno bai taba cewa yana neman shugabancin Najeriya ba.
Sautin ya bayyana Shettima da Amosu na koyin Sultan Sa'ad Abubakar III da Shugaba Buhari da kuma Rotimi Amaechi. Gusau yace wanda ya kawaikwayi Shettima ya manta Shettiman nada lankwasar harshe irin na Kanuri. Yana kuma magana a hankali ne ba da sauri ba.
Wasu da aka zanta dasu sun ce muryoyin da suka ji basu yi kama da na Shettima ko Amosun ba.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Facebook Forum