Wani kwararre, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce sun sha gani a kasashe irin Saliyo da Liberiya, inda ake amfani da yara wajen aikata kunar bakin waken. Ya ce a Saliyo ya ga yara ‘yan shekaru biyar da bakwai da kuma dan shekara goma. Ya ce ya na ganin ana amfani da su ne saboda rashin wayonsu na iya daukar matakin hana kansu shiga wannan aikin ba. Ya ce akwai kuma wata hikima ko hisirin da su ke yi ma yaran. Ya ce wani sa’in da an kama yaran sai kawai a masu sihiri ta yadda ba za su ji sha’awar komai ba sai kisan kai. Ya ce ya shaidi haka ma a Saliyo game da wasu daga cikin yaran da aka kama.
Ya ce wasu daga cikin yaran da su ka koma hayyacinsu, sun bayyana cewa ana ba su wasu jiko ne da kan sa su jib a su sha’awar komai sai yanke mutane ko harbe mutane da sauransu. Ya ce yaran da su ka zakulo bayanai daga garesu a Saliyo sun ce ba su ma san iya mutanen da su ka kashe ba saidai kawai ya gafarce su. Ya ce a yanzu su na ganin ba mamaki ma wasu daga cikin yaran da aka kama a Chibok ne ake amfani da su wajen kai harin.
Da wakilinmu ya tambaye shi yadda za a iya gane wadanda su ka zo kaddamar da harin kunar bakin wake sai ya ce, za ka ga cewa mutum ko da ma ba lokacin zafi ba ne sai ya yi ta zufa, ya na wani wari – au na turare shi da aka yi, au na wani maganin da aka ba shi. Za ka kuma ga idanunsa sun yi ja saboda abin da aka bas hi ya sha ko kuma halin tashin hankali da yake ciki. Sannan idan an lura sosai za a ga alamar cewa ya yi nauyi fiye da kima ko kuma wasu sassansa na nuna alamomin mai dauke da wasu abubuwa na ba saban ba. Za kuma ka ga cewa babu ruwansa da sauraron komai, shi dai kawai ya kai ga wurin da aka tura shi. Idan kuma a mota ne z aka ga cewa motar ta dan yi kasa saboda bama-baman da akan hada a gida na da nauyi sosai. Ya ce da an ga irin wadannan alamomin kar a kusanci mutum; a kira jami’an tsaro tunda su ke da kwarewa kan al’amarin.