Wata motar daukan kaya shake da bamabamai ta tarwatse a wata makarantar hors da 'yansanda dake yammacin kasar Libya.
Rahotanni daga kasar sun ce akalla mutane hamsin ne suka rasa rayukansu a makarantar yayinda dubbai suka jikata kamar yadda wasu jami'ai da 'yan jaridan wurin suka sanar.
Bam din ya fashe ne yayinda daruruwan kuratan 'yansanda suka hallara a garin Zilten domin samun horo. Yanzu dai mutane 50 sun sheka lahira da kyautata zaton adadin ka iya haurawa zuwa 65 ko fiye ma da hakan.
Kawo yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin.
Kasar ta Libya dai ta dare gida biyu tsakanin masu tsatsauran ra'ayin addinin Islam da suka kwace babban birnin kasar Tripoli da kuma gwamnatin kasar da kasashen duniya suka amince da ita wadda ta arce zuwa Tobruk inda take gudanar da nata mulkin.
Watan jiya ne bangarorin biyu dake fafatawa da juna suka rabtaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya duk da tababar dake akwai akan halarcin yarjejeniyar.
Libya ta shiga rikicin kabilanci da na siyasa tun lokacin da aka hambare gwamnatin mulkin kama karya ta Moammar Gadhafi wanda aka kasheshi a shekarar 2011