Inda aka kai hari yana da nesar kilomita daya kacal ne da kan iyakar Nijer da Najeriya kuma kilomita kasa da goma zuwa hedkwatar gundumar Birnin Konni na Jamhuriyar Nijer.
Maharan sun je neman wani attajiri ne mai suna Badamasi wanda Muryar Amurka ta tattuna dashi kuma ya bayyana muna yanda wannan lamarin ya faru.
Wannan lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomi suka maida hankali sosai a kan wannan iyakar bayan a wasu kwanakin da suka shude aka lura da wadansu jama'a da suka soma bayyana wasu dabi'u da hukumomi suka ce ba za su lamunta da su ba, har ma ta kai ga gudanar da taron gaggawa a kan a jahohinn Tahoua da Dosso daga Nijer da Sokoto daga Tarayar Najeriya.
Wakilin Muryar Amurka a yankin ya nemi sani ko maharani sun yiwa mutane lahani yayin wannan harin a garin Rungumawar Jawo, Alhaji Badamasi da maharani suka je nema yace an taba lafiyar matarsa a cikin wannan harin.
Mutanen da suka kubuta da kiar daga hannun wadanan miyagun sun ce, su gaya musu cewa za su koma a garin na Rungumawar Jao nan da dan kankanan lokaci.
Ga rahoton da Harouna Mamane Bako ya aiko mana:
Facebook Forum